Ƴan Najeriya na shirin sake komawa rumfunan zaɓe a watan Janairun 2027, inda miliyoyin masu kaɗa ƙuri’a za su zaɓi shugaban ƙasa, gwamnoni, da kuma ƴan majalisun tarayya da na jihohi.
A zaɓen 2023, mutane da dama sun sa ran cewa amfani da sabbin fasahohi a zaɓe, yawan fitowar matasa kaɗa ƙuri’a da kuma zazzafar takara tsakanin manyan ƴan takara uku za su ƙara ƙarfafa dimokuraɗiyyar Najeriya.
Sai dai matsalolin da aka samu daga hukumar zaɓe ta INEC na rashin nuna sakamakon zaɓe ta intanet (IReV) sun haifar da shakku kan sahihancin zaɓen a idanun mutane da dama.
An ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar. Sai dai manyan abokan hamayyarsa, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP, sun ƙalubalanci sakamakon a kotu, amma Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Tinubu.
Bayan shafe shekaru uku, an ga sauye-sauye dama a fagen siyasa da tattalin arziki Najeriyar. An samu sauye-sauyen dokokin zaɓe, jam’iyyar APC ta ƙara faɗaɗa tasirinta a siyasance, yayin da ƴan ƙasar ke ci gaba da ƙorafi kan tsadar rayuwa, rashin tsaro da matsalar wutar lantarki.






